Hauza/ A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah Muhammad (S), an gudanar da wata gagarumar muzaharar Mauludi a garin Gwandu da ke Jihar Kebbi da kuma garin Kauran Namoda a jihar Zamfara Najeriya, inda dimbin al’ummar Musulmi suka fito domin nuna farin cikinsu da zagayowar wannan rana mai albarka.
A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da muzaharar ne a ranar Laraba, 9 ga Satumba 2026, tare da halartar dattawa, malamai, matasa, yara da sauran al’umma.
Muzahararorin sun gudana cikin natsuwa, tsari da lumana, inda mahalarta suka bayyana farin cikinsu da zagayowar watan da aka haifi Manzon Allah (S), tare da nuna kauna da girmamawa ga Manzon Rahama (S).
Wannan gagarumin taro ya kasance wata dama ga al’ummar Musulmi ta bayyana farin ciki da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (S), tare da tunawa da matsayinsa da koyarwarsa a tsakanin al’ummar Musulmi.
Ga hotunan yadda muzahararorin suka gudana.









Ra'ayinka